Aisha Buhari mace ce mai matukar mutunci – Kakakin Atiku

Aisha Buhari mace ce mai matukar mutunci – Kakakin Atiku

- Kakakin kungiyar kamfen din Atiku Abubakar,ya bukaci Aisha Buhari, da ta ambaci sunayen mutanen da take zargin suna tafiyar da gwamnatin Buhari

- Ya bayyana Aisha Buhari a matsayin “mace mai matukar mutunci” a wannan gwamnatin

- Sowunmi yace Buhari bai iya yaki da rashawa duk da cewar yana da manufar son aikata hakan

Kakakin kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Segun Showunmi ya bukaci uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, da ta ambaci sunayen mutanen da take zargin suna tafiyar da gwamnatin Najeriya don hana shugaban kasar kyawawan ayyukan da yayi niya.

Showunmi wanda yayi Magana da manema labarai a Abeoku, babbar birnin jihar Ogun ya bayyana Aisha Buhari a matsayin “mace mai matukar mutunci” a fannin mulki.

Aisha Buhari mace ce mai matukar mutunci – Kakakin Atiku

Aisha Buhari mace ce mai matukar mutunci – Kakakin Atiku
Source: Depositphotos

Kakakin dan takarar shugaban kasar na PDP yace Buhari bai san yadda ake yaki da rashawa ba duk da cewar yana son yi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari

Showunmi wanda ya kasance dan takarar dan majalisa na kudancin Abeokuta, yace Atiku na da ikon yakar rashawa ta hanya maddawaniya fiye da shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel