Ka zargi kanka a kan rashin cimma nasarar yaki da rashawa - Atiku ga Buhari

Ka zargi kanka a kan rashin cimma nasarar yaki da rashawa - Atiku ga Buhari

A jiya Laraba, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo dangane da rashin cimma nasararsa kan yakar cin hanci da rashawa a Najeriya.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na ja'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce kada shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya zargi kowa dangane da gazawarsa da ta yi sanadiyar rashin cimma nasarar yaki da rashawa a fadin kasar nan face kansa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari na ci gaba da dora alhakin rashin cimma nasarar yaki da rashawa ta gwamnatin sa akan dabaru da kuma tsare-tsaren kasar nan.

Tsohon mataimakin shugaban kasar cikin wata sanarwa a jiya Laraba, ya yabawa gaskiyar shugaba Buhari ta fitowa kuru-kuru wajen bayyana rashin nasarar gwamnatin sa akan yakar cin hanci da rashawa.

Ka zargi kanka a kan rashin cimma nasarar yaki da rashawa - Atiku ga Buhari

Ka zargi kanka a kan rashin cimma nasarar yaki da rashawa - Atiku ga Buhari
Source: Twitter

Sai dai Turakin na Adamawa bai amince da zargin shugaba Buhari ba kan cewa tsare-tsaren kasar nan ke da alhakin yiwa gwamnatin sa shamaki da cimma nasarar tsarkake ta daga duk wani nau'i na cin hanci da rashawa.

Atiku ya yarda cewa akwai kalubalai a tsare-tsaren kasar nan, sai dai hakan bai da wani tasiri ga ingataccen salon gudanar da mulki na siyasa, wanda ko shakka ba bu shine nakasun gwamnatin shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta wawushe $322m da aka kwato a hannun Barayin gwamnati - PDP

Tsohon jami'in hukumar hana fasakauri ta kasa ya kuma hikaito yadda tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya ribaci tsare-tsaren kasa wajen yakar cin hanci da rashawa kan barayin gwamnati musamman tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda, Tafa Balogun, da sauran miyagun ma'aikatan gwamnati.

Ya kara da cewa, ba bu wata matsala a fadar Villa face shugaba Buhari, da kawowa yanzu ya gaza tunkarar makusanta da kuma makarraban gwamnatin sa masu yiwa tattalin arzikin ta'annati wajen yashe dukiyar al'umma iya son ran su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel