Zaben 2019: Dalilin da yasa Buhari zai samu goyon bayan jihar Akwa Ibom - APC

Zaben 2019: Dalilin da yasa Buhari zai samu goyon bayan jihar Akwa Ibom - APC

- Jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom ta ce baiwa wasu 'yayan jihar mukamai a hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya, zai sa Buhari ya samu goyon bayan jihar

- Jam'iyyar ta ce tuni ta shirya kaddamar da yakin zaben dan takarar shugaban kasa a filin wasanni na Godswill Akpabio da ke Uyo

- Haka zalika, rahotanni daga jama'ar jihar Akwa Ibom na nuni da cewa suna cike da doki da shaukin marabtar shugaban kasa Buhari

Jam'iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom, ta ce baiwa wasu 'yayan jihar mukamai a hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya, da kuma gine gine da ake gudanar jihar, karkashin gwamnatin APC mai ci a yanzu, ya bayyana karara dalilin da yasa shugaba Buhari ya samu gagagrumin goyon baya daga al'ummar jihar.

Babban daraktan hukumar shiyyoyi marasa mai da iskar Gas (OGFZA), Mr Umana Okon Umana wanda ya bayyana hakan, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Uyo, ya ce jam'iyyar tuni ta shirya kaddamar da yakin zaben dan takarar shugaban kasa a filin wasanni na Godswill Akpabio da ke Uyo.

Umana wanda shine shugaban babban kwamitin tsare tsare na yakin zaben shugaban kasar ya ce kaddamar da yakin zaben dan takarar shugaban kasar zai tabbatar da irin goyon bayan da Buhari ke samu daga a'lummar jihar.

KARANTA WANNAN: Fadar shugaban kasa ga 'yan Nigeria: Kuyi hattara da jam'iyyar makaryata ta PDP

Zaben 2019: Dalilin da yasa Buhari ya samu goyon bayan jihar Akwa Ibom - APC

Zaben 2019: Dalilin da yasa Buhari ya samu goyon bayan jihar Akwa Ibom - APC
Source: Facebook

Ya ce: "Zuwa yanzu, rahotannin da muke samu daga mambobinmu a fadin Akw1a Ibom, da sauran jihohin Nigeria, na nuni da cewa babban filin wasannin zai cika ya batse a wannan rana ta kaddamar da yakin zaben."

"Haka zalika, rahotanni daga jama'ar jihar Akwa Ibom na nuni da cewa suna cike da doki da shaukin marabtar shugaban kasa Buhari. Hakan kuwa ya tabbatar da irin goyon bayan da zasu taru su yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel