Babu wasu jami’ai da suka tsere kan yaki da Boko Haram – Hukumar yan sanda

Babu wasu jami’ai da suka tsere kan yaki da Boko Haram – Hukumar yan sanda

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta karyata rahotannin cewa jami'anta sun tsere daga yankin arewa maso gabas

- Ta ce dukkan jami'an ta 2000 na can yankin suna aikin da aka tura su yi

- Da ma dai an tura jami'an ne domin su hada gwiwa da sojoji wurin fatattakar 'yan Boko Haram

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafofin watsa labarai na cewa jami'anta sun tsere daga yankin arewa maso gabas inda ake yaki da Boko Haram.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Jimoh Moshood ya aike wa manema labarai ta ce dukkan jami'an ta 2000 na can yankin suna aikin da aka tura su yi.

A baya dai mun samu rahoto daga jaridar Premium Times cewa jami’an yan sanda 167 sun tsere daga filin daga.

Babu wasu jami’ai da suka tsere kan yaki da Boko Haram – Hukumar yan sanda

Babu wasu jami’ai da suka tsere kan yaki da Boko Haram – Hukumar yan sanda
Source: Depositphotos

"Wannan labari kanzon kurege ne kuma yunkuri ne na yin tarnaki kan jajircewar da 'yan sanda ke yi wurin yakar ya ta’addan Boko Haram", in ji kakakin rundunar.

KU KARANTA KUMA: Zambar N2.5b: DSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari ga ‘Yan sanda

Da ma dai an tura jami'an ne domin su hada gwiwa da sojoji wurin fatattakar 'yan Boko Haram.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel