Gwamnatin Tarayya ta wawushe $322m da aka kwato a hannun Barayin gwamnati - PDP

Gwamnatin Tarayya ta wawushe $322m da aka kwato a hannun Barayin gwamnati - PDP

Za ku ji cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta bankado wata kitimurmura gami da muguwar ta'ada da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar sa ta APC ke faman aiwatarwa a fadin kasar nan ba tare a masaniyar daukacin al'umma ba.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar PDP na zargin fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da yaudarar al'umma wajen wawushe kudaden da aka kwato hannun baryin gwamnati na kimanin dalar Amurka miliyan 322, da ya yi daidai da Naira biliyan 115.

Jam'iyyar PDP na zargin gwamnatin shugaba Buhari da yin basajar rabawa talakawan Najeriya ta hanyar shirin nan na TraderMoni domin wawushe dukiyar kasa da ta kwato hannu barayin gwamnati.

Kazalika jam'iyyar ta zargi gwamnatin tarayya da wawushe Naira Biliyan 4 ta hanyar basaja da shirin TraderMon da kuma shirin nan na bayar da tallafi ga Manoma tare da hadin gwiwar babban bankin Najeriya domin yakin neman zaben shugaba Buhari na zaben badi.

Kola Ologbondiyan

Kola Ologbondiyan
Source: Facebook

Wannan babban zargi na aikata muguwar ta'ada da zaluntar al'ummar Najeriya ya sanya jam'iyyar PDP ke kira ga hukumar hana yiwa tattalin arziki ta'annati ta EFCC, akan gaggauta bincikar lamarin domin tabbatar da gaskiyar sa.

Babban sakataren hulda da al'umma na jam'iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, shine ya yi wannan kira cikin wata sanarwa a jiya Laraba. Ya nemi hukumar EFCC ta fara gudanar da bincike kan dukkanin 'yan majalisar wakilai masu hannu cikin wannan lamari da kuma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da suka damalmala cikin zargin.

KARANTA KUMA: Ababe 5 da ya kamata shugaba Buhari ya kudirta domin nasara a zaben 2019

Mista Kola ya zargi 'yan majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa da karkatar da akalar Naira Biliyan 33 na kudaden kayan masarufi da kuma jin dadin 'yan gudun hijira da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya kara da cewa, ba bu jin kai ko tausayi a zuciyar shugaba Buhari dangane da furucin sa na cewa, al'ummar Najeriya su sake daura damarar fuskantar matsananciyar wahala a shekarar badi yayin da gwamnatin sa ke fama tatse masu dukiya domin cimma manufar sa ta yakin neman zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel