An kama yan sanda 4 da lafin fashi a Lagas

An kama yan sanda 4 da lafin fashi a Lagas

- An kama jami’an yan sanda hudu da ke aiki a tashar Ijanikin da ke jihar Lagas bisa zargin yiwa wani mai suna Theodore Ifunnaya fashin kudi 350,000 CFA (kimanin N221,508)

- Wanda aka yiwa fashin dan Najeriya ne mazaunin kasar Togo inda ya dawo bikin Kirsimeti

- A yanzu haka jami’an na tsare inda ake bincikarsu kuma za’a kore su idan har aka same su da laifi

Rahotanni sun kawo cewa an kama wasu jami’an yan sanda hudu da ke aiki a tashar Ijanikin da ke jihar Lagas bisa zargin yiwa wani mai suna Theodore Ifunnaya fashin kudi 350,000 CFA (kimanin N221,508).

Chike Oti, kakakin yan sandan jihar Lagas, yace wanda aka yiwa fashin dan Najeriya ne mazaunin kasar Togo.

Oti yace jami’an yan sandan za su fuskanci hukuncin kora idan har aka kama su da laifi, amma ya kara da cewa ba’a yiwa wanda abun ya shafa tsirara ba a lokacin tambayoyi kamar yadda ake zargi a wasu wurare.

An kama yan sanda 4 da lafin fashi a Lagas

An kama yan sanda 4 da lafin fashi a Lagas
Source: Depositphotos

Ya ce an mika yan sandan da abun ya shafa zuwa ga sashin bincike na rundunar domin gudanar da bincike a kansu.

Anyi zargin cewa jami’an sun tsare mutumin ne da ya fito daga Togo don bikin Kirsimeti a Najeriya a yankin Iyana-Ira, Badagry a ranar 17 ga watan Disamba.

Sai suka fara incikar mutumin tare da yi masa tambayoyi, inda anan suka gano kudin a tare da shi.

Anyi zargin cewa sun dauko shi a motar sintirinsu zuwa ofishin yan sandan Ijaniki inda anan ne suka kwace kudin daga hannunsa sannan suka kira wani mai chaji domin mayar da kudin zuwa naira.

K KARANTA KUMA: Da ban goya ma Buhari baya ba a 2015 da bai lashe zabe ba - Obasanjo

Bayan sun yi masa barazana, sai suka sake shi sannan suka bashi N2000 cikin kudinsa, domin ya samu damar zuwa gidansa a Lagas.

Bayan ya samu yanci daga yan sandan, sai ya fada ma yan’uwansa halin da ya shiga wanda ya kai ga aka shigar da kara wa Hope Okafor, kwamandan yankin ‘K’.

Kwamandan, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan yan sanda ya shiga lamari sannan ya kwato kudin da suka sace sannan kuma aka kama yan sandan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel