Har in mutu, Buhari zai ci gaba da kirana 'Sir' - Obasanjo ya maida martani

Har in mutu, Buhari zai ci gaba da kirana 'Sir' - Obasanjo ya maida martani

- Chief Olusegun Obasanjo, ya ce ya cancanci ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, kasancewar shima ya shugabanci kasar a lokuta daban daban

- Ya ce har ya mutu Buhari zai ci gaba da kiransa da 'Sir'

- Olusegun Obasanjo ya kuma shawarci Gwamna Amosun na jihar Ogun da ya kauracewa shiga shirgin Buhari, yana mai cewa su biyun sojoji ne

Tsohon shugaban kasar Nigeria, Chief Olusegun Obasanjo, a ranar Laraba, ya ce ya cancanci ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, kasancewar shima ya shugabanci kasar a lokuta daban daban.

Ya bayyana hakan ne a taron bukin ranar Ibogun ta shekarar 2018 wanda ya samu halartar wasu jigogi a jihar, da suka hada da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun, dan takarar kujerar gwamnan jihar daga jam'iyyar ADC, Prince Gboyega Nasir Isiaka da takwaransa na jam'iyyar APM, Hon. Adekunle Akinlade.

Olusegun Obasanjo ya kuma shawarci Amosun da ya kauracewa shiga shirgin Buhari, yana mai cewa su biyun sojoji ne.

KARANTA WANNAN: Atiku ya bukaci a gaggauta binciken iyalan Buhari kan mallakar Etisalat da bankin KeyStone

Har in mutu, Buhari zai ci gaba da kirana 'Sir' - Matsayar Obasanjo ya maida martani

Har in mutu, Buhari zai ci gaba da kirana 'Sir' - Matsayar Obasanjo ya maida martani
Source: Twitter

Ya ce: "Na san Buhari shima ya sanni. Har in mutu, Buhari zai ci gaba da kirana 'Sir'. A 2015, idan da har ban goyi bayan Buhari ba, to kuwa da ya fadi zabe. Ina da abubuwan da zasu gyara masa kuskurensa. Bai kamata Nigeria ta kasance a halin da take ciki yanzu ba. Nigeria na iya fin haka. Allah ya bamu dukkanin abubuwan da ake bukata na samun ci gaba.

"Na cancanci kalubalantar Buhari. Na daya, na yi hakan a baya. Na biyu, na sadaukarda rayuwata ga wannan kasar. Hatta dan da na haifa shima ya zubar da jininsa ga wannan kasar. Don me ba zan iya yin magana akan abun da yafi dacewa da kasar nan ba? Tabbas, na cancanci yin hakan."

Dangane da zaben gwamnan jihar a 2019, tsohon shugaban kasar ya ce har kullum zabin Allah shine mafi dacewa kan wanda zai zama gwamnan jihar, tunda shi ba ruwansa da ko kai waye, arzikinka ko jam'iyyarka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel