Zambar N2.5b: DSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari ga ‘Yan sanda

Zambar N2.5b: DSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari ga ‘Yan sanda

- Hukumar DSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari, Sani Baba Inna da ke tsare a hannunta ga hukumar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike

- Ana dai zarginsa ne da yin zambar wasu makudan kudade day an siyasa da manyan yan kasuwa ke ba uwargidan shugaban kasar kyauta

- A yanzu dai yana a hannun yan sanda inda za su bincike shi

Hukumar tsaro na DSS ta sakar ma yan sanda mai tsaron Aisha Buhari, Sani Baba Inna da ke tsare a hannunta domin su ci gaba da bincikensa akan zargin zambar biliyoyin naira da ya yi daga cikin kyaututtukan da ake ba uwargidan Shugaban Kasar.

An dai tsare Baba Inna ne kan zargin amsar kudade daga hannun ‘yan siyasa da wasu manyan ‘yan kasuwa da suka yi wa uwargidan shugaban Kasa Aisha kyauta, kudade da yawansu ya kai sama da naira biliyan 2.

Zambar N2.5b: DSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari ga ‘Yan sanda

Zambar N2.5b: DSS ta mika mai tsaron Aisha Buhari ga ‘Yan sanda
Source: Facebook

Ko da aka fara gudanar da wannan bincike an gano cewa babu irin wadannan kudade a asusun ajiyar sa amma duk da haka jami'an DSS suka tasa keyar sa inda sai yanzu suka sake shi.

A wancan lokaci an gano cewa rundunar ‘yan sanda sun gudanar da bincike akai kuma ba a same shi da laifi ba.

Hakazalika ita kanta uwargidan shugaban kasar a wasika da ta rubuta ta bayyana cewa daga ofishin ta wanda hadiminta kan harkokin yada labarai Suleiman Haruna ya saka wa hannu ta ce, Sani wanda ya fara aiki da ita tun a 2016 ya rika a amfani da sunan ta wajen karbar kyaututtuka wajen mutane.

Ta ce tana da masaniya game da munanan abubuwan Sani amma kama shi da jami’an tsaro suka yi ne ba ta sani ba.

KU KARANTA KUMA: Da ban goya ma Buhari baya ba a 2015 da bai lashe zabe ba - Obasanjo

Daga nan Aisha ta kuma tabbatar da cewa ita ko ‘ya’yan ta basu taba aika wani ma’aikaci ya karbo musu alfarma ta kowacce iri daga hannun wani ba.

Yanzu dai ‘yan sanda zasu ci gaba da bincike akan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel