Da ban goya ma Buhari baya ba a 2015 da bai lashe zabe ba - Obasanjo

Da ban goya ma Buhari baya ba a 2015 da bai lashe zabe ba - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba don ya marawa shugaba Buhari baya a shekarar 2015 da bai kai labara ba a zabe

- Obasanjo yace ya isa ya yi wa Buhari Magana idan yayi ba daidai ba domin shima ya rike mukamai daban-daban a kasar

- Yace bai kamata ace har yanzu kasar na nan a yadda take a yanzu ba

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a ranar Laraba, 26 ga watan Disamba ya bayyana cewa a shekarar 2015, idan da a ce bai marawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya ba da bazai kai labari ba kamar yadda ya bayyana cewa shine mutun da yafi cancanta ya soki shugaba Buhari, saboda ya jagoranci lamuran kasar lokuta daban-daban.

Da ban goya ma Buhari baya ba a 2015 da bai lashe zabe ba Obasanjo

Da ban goya ma Buhari baya ba a 2015 da bai lashe zabe ba Obasanjo
Source: Depositphotos

Obasanjo yayinda yake jawabi a biki ranar Ibogun na 2018 tare da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun da sauran mutanen da suka hallara yace: “Na san Buhari shima kuma ya san ni. Har zuwa ranar mutuwa na, Buhari zai ci gaba da kirana a matsayin ‘yallabai’. A 2015, da ban marawa Buhari baya ba, da bai ci zabe ba. Ina da abunda ya cancanta wajen gyara masa idan yayi ba daidai ba bai kamata Najeriya ta kasance a yadda take a yanzu ba. Naeriya na iya fin haka. Allah ya bamu duk abunda muke bukata.

“Na cancanci yin adawa da Buhari. Da farko, Nayi shugabanci a baya. Na biyu, na sadaukar da jinina ga kasar nan. Har dan cikina ya sadaukar da jininsa. Me zai hana nayi Magana do ci gaban kasar? Na cancanci yin haka."

KU KARANTA KUMA: Cacar bakin da ake yi tsakanin Aisha Buhari da Shugaban kasa ya sabawa musulunci - Inji Balarabe Musa

Ya ci gaba da fadin: “Nayi farin ciki kan cewa gwamnan, Ibikunle Amosun yayi Magana dake adawa da rikici. Ina so na fada maku, idan baka hana rikici a tsakanin magoya bayanka ba,da kanka zaka yi kuka, babu wani dalili na siyasar daba a jihar.

“Na yi zabi na, ba lallai yayi daidai da naka ba. Ka bari zabina ya zama nawa sannan zabinka ya zama naka sannan a bari Allah ya yanke hukunci sannan duk wanda yayi nasara namu shine mu mara masa baya,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel