Ba na jin dadin ganin yadda halin da APC ta shiga – John Oyegun

Ba na jin dadin ganin yadda halin da APC ta shiga – John Oyegun

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun yayi hira da jaridar Daily Trust kwanan nan inda yayi magana game da zaben 2019, tazarcen Buhari da kuma halin da APC ta ke ciki.

Ba na jin dadin ganin yadda halin da APC ta shiga – John Oyegun

John Oyegun yace Shugaba Buhari ya fi kowa cancanta da mulki
Source: UGC

Tsohon shugaban jam’iyyar mai mulki ya nemi ‘yan siyasa su guji raba kan al’umma, su tsaya su yi yakin neman zabe na gaskiya. Oyegun wanda ya sauka daga kujerar sa kwanaki yayi kira ga Matasa su guji rigimar siyasa a badi.

Odigie Oyegun ya tabbatar da cewa akwai baraka yanzu a tafiyar APC, amma ana kokarin shawo kan wadannan matsaloli kafin zabe. Oyegun yace yana cikin wadanda su ke kokarin ganin an yi sulhu a wasu Jihohin da ake rikici.

Cif John Oyegun ya kuma bayyana cewa Buhari ne ya fi kowa dacewa ya rike kasar nan har zuwa 2023. Tsohon gwamnan na Jihar Edo yace a na sa ganin, Buhari ya fi sauran ‘yan takarar cancantar rike kujerar shugaban kasa a Najeriya.

KU KARANTA: Makiyayan Najeriya za su marawa Buhari baya a zaben 2019

A wannan doguwar hirar da aka yi, John O. Oyegun yayi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa yana shirin ficewa ya bar APC. John Oyegun yace su ne su kafa jam’iyyar APC, har ya zama shugaban ta, kuma su ka kafa gwamnati.

Oyegun ya nuna cewa bai jin dadin abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar inda ake samun rabuwar kai a cikin gida. A irin su Ogun da Imo, gwamnonin Jihohin ba su tare da ‘yan takarar da APC ta tsaida, wanda yace hakan yana masu ciwo.

Dattijon ‘Dan siyasar dai ya bayyana cewa yanzu haka ana kokarin dinke barakar da ta shigo jam’iyyar tun bayan tsaida ‘yan takaran 2019. Oyegun yace yana cikin masu kokarin ganin an yi sulhu musamman a Jihohin kudancin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel