Atiku ya bukaci a gaggauta binciken iyalan Buhari kan mallakar Etisalat da bankin KeyStone

Atiku ya bukaci a gaggauta binciken iyalan Buhari kan mallakar Etisalat da bankin KeyStone

- Atiku Abubakar, ya bukaci a ta gaggauta fara bincike kan mamallakan babban kamfanin sadarwa na Etisalat Nigeria da kuma bankin Keystone

- Rahotanni sun bayyana cewa akwai wasu iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke da hannun jarin $2bn a Etisalt Nigeria

- Haka zalika, akwai zargin cewa wasu daga cikin iyalan shugaban kasar, na da hannun jarin N307.5bn a bankin Keystone da N3bn a Pakistani Islamic Bank

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta fara bincike kan mamallakan babban kamfanin sadarwa na Etisalat Nigeria da kuma bankin Keystone.

A cikin wata sanarwa, wacce Phrank Shaibu, daya daga cikin hadimansa ya rabawa manema labarai a madadinsa, Atiku ya ce kiran ya zama wajibi ne biyo bayan rahotannin da ke yawo na cewar wasu daga cikin iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari na da hannun jari mai tsoka a Etisalat Nigeria, da suka kai kimanin $2bn.

Shuaibu ya kalubalanci mahukunta da su gudanar da kwakkwaran bincike kan wannan zargi, kana su bayyanawa jama'a sakamakon binciken nasu.

KARANTA WANNAN: Ranar hisabi: An yiwa Saraki ihu a wurin gangamin kamfe a garin Ilori (Bidiyo)

Atiku ya bukaci a gaggauta binciken iyalan Buhari kan mallakar Etisalat da bankin KeyStone

Atiku ya bukaci a gaggauta binciken iyalan Buhari kan mallakar Etisalat da bankin KeyStone
Source: Facebook

"Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran mahukunta dasu gaggauta soma bincike don gano boyayyun fuskokin mamallakan Etisalat Nigeria, da kuma bankin Keystone," a cewar sanarwar.

"Haka zalika, Atiku ya bayyana kaduwarsa kan wani rahoto da ya samu daga majiya mai tushe lan cewar iyaln shugaban kasar na cikin fannin kudin kasar dumu dumu, bayan mallakar hannun jari mai tsoka a bankin Keystone na kudi har $1.916bn (dai dai da N307.5bn) da kuma hannun jarin akalla N3bn a sabon bankin Pakistani Islamic Bank."

Ya kuma kalubalanci shirin baiwa manoma rance na Anchor Borrowers wanda gwamnatin APC ta bullo da shi karkashin babban bankin Nigeria CBN, da cewar an bullo da shirin ne don sayen kuri'un masu cin gajiyar shirin.

Atiku ya gargadi Buhari akan kauracewa amfani da kudaden kasa wajen yakin zabensa a 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel