Kwara: Gwamna Ahmed ya yi Allah-wadai da lalata allunan tallar jam'iyyu da 'yan takararsu

Kwara: Gwamna Ahmed ya yi Allah-wadai da lalata allunan tallar jam'iyyu da 'yan takararsu

- Gwamna Ahmed na jihar Kwara, ya yi Allah-wadai da lalata alluran yan takara da jam'iyyunsu a fadin jihar

- Magoya bayan Sanata Bukola Saraki da na dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq, sun yi gaba da gaba a Ilorin

- A yayin da Abdulrazaq ke zargin jam'iyyun hamayya da gurbata tsarin siyasa, ita kuma PDP ta ce shi ne silar faruwar duk wani abu mummuna a siyasar jihar

A ranar Laraba, Gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed, ya yi Allah-wadai da wata mummunar dabi'a da wasu da ba a san ko suwanene ba suke aikatawa, na lalata allunan tallar 'yan takara da jam'iyyun siyasarsu a fadin jihar, wanda ya bayyana hakan a matsayin abun takaici wanda ba zai samu gurbi a iihar ba.

Magoya bayan shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki da na dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq, sun yi gaba da gaba a Ilorin, a ranar 25 ga watan Disambar 2018 a wani taron shekara shekara na tallafawa gidauniyar kungiyar bunkasa magadan sarakunan Ilorin (IEDPU), wanda ya jawo hatsaniya tare da kawo karshen taron.

Masu shirya taron sun gayyaci Abdulrazaq zuwa wajen taron don sanar da tashi gudunmowar, a sa'ilin ne kuma magoya bayan abokan hamayyar biyu sukayi gaba da gaba, wanda ya tilasta jami'an tsaron Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari gaggauta dauke shi daga wajen taron, ganin yadda lamarin ke kara rincabewa.

KARANTA WANNAN: Ranar hisabi: An yiwa Saraki ihu a wurin gangamin kamfe a garin Ilori (Bidiyo)

Kwara: Gwamna Ahmed ya yi Allah-wadai da lalata allunan tallar jam'iyyu da 'yan takararsu

Kwara: Gwamna Ahmed ya yi Allah-wadai da lalata allunan tallar jam'iyyu da 'yan takararsu
Source: Depositphotos

Haka zalika, kusan dukkanin wasu alluran tallar dan takarar na jam'iyyar APC, da aka kafa su a wasu muhimman wurare a Ilorin, an lalata su.

A yayin da kungiyar yakin zaben Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq suke zargin jam'iyyun hamayya da gurbata tsarin siyasa, ita kuma jam'iyyar PDP a cikin wata sanarwa daga Tunde Ashaolu, ta ce Abdulrazaq ne silar faruwar duk wani abu mummuna a siyasar jihar.

Sai dai, Gwamna Ahmed a cikin wata sanarwa daga mai tallafa masa na musamman kan kafofin sadarwa da watsa labarai, Dr. Muyideen Akorede, ya yi Allah-wadai da lalata alluran yan takara da jam'iyyunsu a jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel