Wajibi ne ku murkushe Boko Haram tunda kun fi su makamai da gogewa – Buratai ga Sojoji

Wajibi ne ku murkushe Boko Haram tunda kun fi su makamai da gogewa – Buratai ga Sojoji

Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya gargadi dakarun sojoji da ke yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas da su yi kaffa-kaffa da farfagandar da ake yadawa a kan yaki da ta’addanci.

A cikin sakon murnar zagayowar Kirsimeti da ya aika wa sojojin a ranar Talata, 25 ga watan Disamba Buratai ya kara nanatawa cewa kokarin da sojojin suka yi ya nuna cewa lallai an samu galaba kan Boko Haram.

Wajibi ne ku murkushe Boko Haram tunda kun fi su makamai da gogewa – Buratai ga Sojoji

Wajibi ne ku murkushe Boko Haram tunda kun fi su makamai da gogewa – Buratai ga Sojoji
Source: Depositphotos

Yace: “Dalili kenan a yanzu suke yada farfagandar karya don su karya muku guiwa suna bayyana irin karfin da suke yi wa jama’a cewa wai su na da shi.

“Amma ya na da kyau sojoji su gane cewa Boko Haram ba wata tsiya ba ce, kawai dai wasu gungun mabartana ne.

“Don haka tilas ku tashi tsaye ku bankado sauran burbishin su da ya rage.

KU KARANTA KUMA: Sanata Arise ya caccaki Buba Galadima, ya ce Buhari ne zai lashe zaben 2019

“Mun fa fi su samun horo da gogewar iya fafata yaki, mun fi su kayan fama kuma mun fi su kwarewa. Kuma mu na da tarihin samun nasarori a fagagen fama a nan gida Najeriya da kuma kasashen waje.”

Buratai ya kuma jinjina musu da gode musu a kan namijin kokarin da su ka yi wajen jajircewa da sadaukar da rayukan su a cikin 2018.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel