Duk 'yan uwan Buhari talakawa yanzu sun biloniyas - Buba Galadima

Duk 'yan uwan Buhari talakawa yanzu sun biloniyas - Buba Galadima

Kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Buba Galadima, ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da azurta 'yan uwa da dangi.

Da yake magana a yau, Laraba, a wani shirin gidan talabijin na Channels, Galadima ya ce daga cikin 'yan uwan shugaba Buhari da basu da komai kafin 2015, yanzu sun mallaki gidaje a garin Daura, jihar Katsina.

Galadima na wadannan kalamai ne a cikin shirin, yayin mayar da martani ga Sanata Ayo Arise dake kare bangaren gwamnati.

"Shugaba Buhari ya yi alkawarin zai gudanar da sahihin zabe a kasar nan kuma kowa ya yarda da shi saboda mutum ne mai kima. Hakan ne ya sa nima nake cikin masu goyon bayan Buhari," a kalaman Sanata Arise.

Duk 'yan uwan Buhari talakawa yanzu sun biloniyas - Buba Galadima

Buba Galadima
Source: Depositphotos

Sai dai Galadima ya ce bai yarda akwai ragowar wata kima a tare da Buhari yana mai bayyana cewar da yawan 'yan uwan Buhari sun zama masu arziki.

"Ni ban ga wata kima da ta rage tattara shugaban kasa ba. Ina kima ga mutumin da ya bar na jikinsa na karbar cin hanci da rashawa. Mun fa san 'yan uwansa, mun san abokansa da talauci ya addaba kafin shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Kirsimeti: Musulumi sun ci sun sha a gidan Fasto a Kaduna, hotuna

"Akwai 'yan uwansa da sai mun basu N2,000 kudin mota kafin su iya ziyartar sa a Kaduna, amma yau sun zama biloniyas. Zan iya nuna su ga duk wanda ke son sanin su, a saboda haka babu wata maganar kima tare da shugaban kasa da kuma wannan gwamnati," a kalaman Galadima.

Sannan ya cigaba da cewa, "kaje unguwar masu kudi a Daura ka gani, duk manyan gidajen da zaka ga an gina su kamar a Landan ko Dubai na 'yan uwan Buhari ne. A daina fada min cewar shugaban kasa na da kima ko gwamnatinsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel