An zargi Gwamnan Bayelsa da yin kama karya a Jam’iyyar PDP

An zargi Gwamnan Bayelsa da yin kama karya a Jam’iyyar PDP

Mun samu labari daga jaridar Vanguard ta kasar nan cewa wasu ‘ya yan PDP a Jihar Bayelsa sun fara nuna alamun za su iya yi wa jam’iyyar bore a zabe mai zuwa na 2019, saboda wasu dalilai irin na su.

An zargi Gwamnan Bayelsa da yin kama karya a Jam’iyyar PDP

'Yan Baissa PDP Progressive sun ce na kusa Gwamna Dickson su na hana ruwa gudu a PDP
Source: Depositphotos

Kungiyar Baissa PDP Progressive ta bayyana cewa a halin yanzu rikicin da ke cikin jam’iyyar PDP na reshen jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudancin Najeriya zai iya cin jam’iyyar a babban zaben da za a gudanar a kasar a 2019.

Mose Akene wanda yana cikin manyan wannan kungiya ta Baissa PDP Progressive ya bayyana hakan, a wani jawabi fa ya fitar Ranar Talatar nan. Akene ya koka da yadda PDP ta tsaida ‘yan takarar ta da za su fafata a zaben badi.

Jagoran wannan kungiya ta PDP, yake cewa mai girma gwamnan jihar Bayelsa da wasu tsirarrun mukarraban sa ne kurum su ka yi abin da su ka ga dama wajen bada tuta a PDP ga masu shirin takara a jihar a zaben na 2019.

KU KARANTA: Rikici ya kaure tsakanin ‘Yan PDP da ‘Yan APC a Ilorin

Mose Akene, a jawabin na sa ya kara da cewa duk da mutanen Bayelsa sun dade su na goyon PDP a siyasar Najeriya, wannan karo za su iya juyawa jam’iyyar da ke mulkin jihar tun 1999 baya a 2019, idan kuwa har aka kai su bango.

Baissa PDP Progressive ta zargi wasu mutane da ake kira 'Yan “restoration caucus” da toyewa al’umma zabin su a tsarin damukaradiyya saboda son rai. Mutanen wannan kungiya su na samun daurin gindi ne daga wajen gwaman jihar.

Shugaban wannan kungiyar ya gargadi gwamnan da mutanen sa su guji yin abin da zai kawo fushin mutane har ta kai su juyawa PDP baya. Akene ya rufe jawabin da cewa jama’a ne ke zaben wadanda su ke so a Bayelsa ba wasu tsirarru ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel