Kama Deji Adeyanju tuggun siyasa ce ba turbar shari’a ba - Saraki

Kama Deji Adeyanju tuggun siyasa ce ba turbar shari’a ba - Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana tsare lauya mai kare hakkin jama’a, Deji Adeyanju a kurkuku a matsayin tuggu da sharrin siyasa ba wai wani mataki na shari’a kamar yadda ake ikirari ba.

Saraki ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawan bayar da umarni domin a saki Adeyanju, saboda ya tabbatar da cewa bai kyale ‘yan sanda su ci gaba da danne wa Adeyanju ‘yancin sa na dan ba.

Wannan kakkausan kira na Saraki na zuwa ne kwanaki shida bayan da majalisar dattawa ta bai wa Kwamitin Majalisa kan Shari’a da Harkokin ‘Yan Sanda mako guda da ya gudanar da bincike kuma ya gano kwamacalar da ta haddasa ‘yan sanda kama Adeyanju har su kai shi Kano a kotu, daga can kuma aka zarce da shi kurkuku.

Kama Deji Adeyanju tuggun siyasa ce ba turbar shari’a ba - Saraki

Kama Deji Adeyanju tuggun siyasa ce ba turbar shari’a ba - Saraki
Source: Depositphotos

An fara kama shi a ranar 28 ga watan Nuwamba, bayan da ya jagoranci masu zanga-zanga a kan nuna fushi da damuwa dangane da yadda manyan shugabannin tsaron kasar nan ke nuna bambanci da son kai a lamura da batutuwan zabe mai zuwa.

Bayan an bayar da belin sa a ranar 6 ga watan Disamba, sai ‘yan sanda suka sake kama shi a kofar kurkukun Keffi, daidai lokacin da ya fito.

KU KARANTA KUMA: Tarin farin ciki a APC yayinda mambobin PDP suka sauya sheka a mahaifar Saraki

An garzaya da shi kotu a Kano a bisa wani abin da ‘yan sanda suka kira sabon binciken da ya taso dangane da wata shari’ar zargin kisa da aka taba yi wa su Deji Adeyanju, wanda aka yi tun lokacin da ya ke karatu a Jami’ar Bayero, Kano.

Idan ba a manta ba, jim kadan bayan kama Deji, lauyan sa a lokacin da aka yi waccan shari’ar, Festus Kiyamo ya fito ya ce Deji ba shi da laifi, kuma a wancan lokacin ma alkali ya wanke, shi ba a same shi da laifi ba.

Kiyamo ya yi wannan furucin ne duk kuma da cewa a yanzu ya na cikin gwamnatin Buhari.

A yanzu dai a na tsare da Adeyanju ne sai cikin watan Fabrairu za a yi maganar beli, domin alkali su na hutun karshen shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel