Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP, Buhari Bala da shugabannin kananan hukumomi 4 sun koma APC a Kebbi

Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP, Buhari Bala da shugabannin kananan hukumomi 4 sun koma APC a Kebbi

- Tsohon ma’ajin jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Buhari Bala da shugannin kananan hukuma hudu na jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC

- Bala ya kuma bayar da gudunmawar wani ofishi da motoci 11 ga kungiyar kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Atiku Bagudu

- Ya yi alkawarin ganin nasarar APC a zabe mai zuwa

Tsohon ma’ajin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Alhaji Buhari Bala da shugannin kananan hukuma hudu na jam’iyyar a ranar Laraba, 26 ga watan Disamba sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Bala ya kuma bayar da gudunmawar wani ofishi da motoci 11 ga kungiyar kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Atiku Bagudu.

Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP, Buhari Bala da shugabannin kananan hukumomi 4 sun koma APC a Kebbi

Yanzu Yanzu: Babban jigon PDP, Buhari Bala da shugabannin kananan hukumomi 4 sun koma APC a Kebbi
Source: Depositphotos

Sun samu tarba daga Gwamna Bagudu da sauran shugabannin APC a Jihar, ciki harda ministan shari’a, Abubakar Malami a wajen kaddamar da kamfen din gwamnan APC wanda aka gudanar a karamar hukumar Argungu da ke jihar wanda ya kasance mahaifar dan takarar gwamnan PDP, Alhaji Isa Galaudu.

Sun kuma tarbi mambobin kungiyar Kwankwasiyya a jihar.

KU KARANTA KUMA: Tarin farin ciki a APC yayinda mambobin PDP suka sauya sheka a mahaifar Saraki

A yake Magana a wajen taron, Bala ya bayyana cewa sun gamsu da tarin nasarorin gwamnatin APC a matakin jiha da kasa baki daya.

Yayi alkawarin aiki domin ganin nasarar sabuwar jam’iyyarsa a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel