Karya Dino yake yi babu wani shiri da muke yi na kama shi da kashe shi – Hukumar yan sanda

Karya Dino yake yi babu wani shiri da muke yi na kama shi da kashe shi – Hukumar yan sanda

- Rundunar yan sandan Najeriya ta karyata shirin kamawa da kashe Sanata Dino Melaye

- Dino dai yayi zargin cewa sufeto janar na yan sanda yayi umurnin kama shi sannan ayi masa alluran mutuwa a ranar Kirsimeti

- Rudunar ta kalubalanci Dino da ya fito yayi magana idan har ya san akwai wani laifi da ya aikata domin ya fuskanci doka

Rundunar yan sandan Najeriya a ranar Laraba, 26 a watan Disamba ta karyata shirin kamawa da kashe Sanata Dino Melaye.

A wata sanarwa daga kakakin yan sanda, DCP Jimooh Moshood yace wani jawabi da Sanata Dino Melaye yayi na cewa “IG na shirn kama shi da yi masa alluranmutuwa,” karya ne.

Moshood yace: “Rundunar ta bayyana cewa jwain makirci ne da kuma haddasa fitina wanda ka iya ba jama’a dariya."

Karya Dino yake yi babu wani shiri da muke yi na kama shi da kashe shi – Hukumar yan sanda

Karya Dino yake yi babu wani shiri da muke yi na kama shi da kashe shi – Hukumar yan sanda
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa: “Babu wani umurni makaancin hakadaga sufeto janar na ya sanda ko wani shiri daga rundunar na kama Sanata Dino Melaye da kuma yi masa alluran mutuwa.”

KU KARANTA KUMA: 2019: Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya – Kungiyar kamfen

Don haka rundunar yan sandan tace: “Idan Sanatan ya sancewa ya aikata wani laifi ko kuma yana sane da kasancewarsa cikin wani laifi, toh ya fito ya bayyana gaskiya sannan ya fuskanci doka maimakon haddasa rudni a tsakanin jama’a.

“Rundunar na kallon hakan a matsayin makirci da haddasa fitina sannan ta karyata zance mai ban al’ajabi da mamamaki da kuma dariya."

Ya kara da cewa Melaye ya kwana da sani cewa jawabinsa laifi ne domin yana iya haddasa rikici a batanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel