Jihohi 6 dake cikin hatsarin fuskantar rikicin zabe - Kungiyar sa-ido ta duniya

Jihohi 6 dake cikin hatsarin fuskantar rikicin zabe - Kungiyar sa-ido ta duniya

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, wata kungiyar kasa da kasa dake sa-ido a kan rigingimu a duniya, tayi gargadin cewar za a iya samun barkewar rikici yayin zaben Najeriya, musamman a wasu jihohi 6.

Kungiyar, maj cibiya kasar Belgium, ta ce gwamnatin zata iya hana faruwar hakan ta hanyar hana amfani da 'yan daba yayin kamfen da kuma inganta tsaro da tattaunawa tsakanin kungiyoyi masu adawa da juna.

A wani bincike da ta ce ta gudanar, kungiyar ta ce rikici na yawan barkewa yayin zabukan Najeriya, musamman daga shekarar 2006 zuwa 2014 inda aka samu barkewar rikici sau 915 tare da asarar rayukan mutane 3,934.

Kazalika, ta bayyana cewar an samu asarar rayuka fiye da 800 a rikicin da ya barke bayan kammala zaben shekarar 2011.

Jihohi 6 dake cikin hatsarin fuskantar rikicin zabe - Kungiyar sa-ido ta duniya

Atiku and Buhari
Source: Twitter

A zaben shekarar 2015, kungiyar ta ce an kashe jimillar mutane 180; 58 kafin zabe da kuma wasu 50 a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyu bayan sanar da sakamakon zabe.

DUBA WANNAN: Kauracewa aiki: Rundunar 'yan sanda ta bayar da umarnin kama jami'anta 190 da aka tura Borno

Yanzu haka kungiyar ta bayyana cewar ta gudanar da wani bincike kuma ta fitar da rahoto mai taken "Nigeria's 2019 Elections: Six states to watch" dake nuna cewar jihohin Ribas, Akwa Ibom, Kaduna, Kano, Filato, da Adamawa na cikin hatsarin fuskantar rikicin zabe.

Duk da silar barkewar rikici a jihohi ta banbanta, kungiyar ta ce akwai manyan sila 4 da ta fuskanci sune a sahun gaba wajen barkewar rikicin.

Abubuwan da kungiyar ta lissafa su ne; zazzafar adawar siyasa dake tsakanin jam'iyyun APC da PDP a jihohin, darajar da jiha ke da ita a sakamakon zaben kasa, hamayya tsakanin tsohon gwamna da mai ci, tasirin kabila da addini a zaben jihohin, da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda da jihohin ke da su, wadanda daga cikinsu ne 'yan siyasa kan dauko hayar 'yan sara suka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel