Sanata Arise ya caccaki Buba Galadima, ya ce Buhari ne zai lashe zaben 2019

Sanata Arise ya caccaki Buba Galadima, ya ce Buhari ne zai lashe zaben 2019

- Sanata Arise ya caccaki Buba Galadima ancewa da yayi Buhari ba zai kai labara ba a zaben 2019

- A cewar sanatan babu tamkar shugaba Buhari a cikin yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasa 2019

- Ya bayyana Galadima a matsayin mutun mai cike da mafarkai

Biyo bayan wani jawabi da Buba Galadima yayi cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai sha kaye a zabe mai zuwa, Sanata Ayodele Arise ya bayar da tabbaci akan cewa shugaban kasar ne zai yi nasara a zaben 2019 mai zuwa.

Arise ya bayyana hakan a wani shirin gidan talbijin din Channels a ranar Laraba, 26 ga watan Disamba 2018.

Legit.ng ta tattaro cewa sanatan, mai wakiltan jihar Ekiti a majalisar dokokin kasar, yace akwai bukatar mutane su yarda da shugaba Buhari sama da kowani dan takara, inda ya kara da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na da shaid na matunci.

Sanata Arise ya caccaki Buba Galadima, ya ce Buhari ne zai lashe zaben 2019

Sanata Arise ya caccaki Buba Galadima, ya ce Buhari ne zai lashe zaben 2019
Source: Depositphotos

Da yake martaniakan jajircwar shugaban kasar na tabbatar da zabe na askiya, Arise ya caccaki Galadima, wanda ya bayyana a matsayin mai mafarki.

Ya kara a cewa koda ba a siga yarjejeniyar zaman lafiya ba, shugaba Buhari da jam’iyyarsa suna nan akan ganin anyi zabe a amana ba tare da rikici ba a 2019.

KU KARANTA KUMA: 2019: Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya – Kungiyar kamfen

A baya dai mun ji cewa Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa ranar 29 ga watan Mayu, 2019 na gabatowa, kuma ba shugaban kasa Muhammadu Buhari za a rantsar ba.

Galadima ya ce zuwa ranar damokradiya mai zuwa a Najeriya, Buhari ya rigada ya mika mulki ga dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel