2019: Yadda Buhari, Osinbajo da Oshiomhole suka yaudari yan Najeriya a ranar Kirsimeti - PDP

2019: Yadda Buhari, Osinbajo da Oshiomhole suka yaudari yan Najeriya a ranar Kirsimeti - PDP

- Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaba Buhari kan wakar Kirsimeti da yayi a matsayin taya kiristoci bikin Kirsimeti

- Buhari yayi wakar Kirsimeti ne tare da Yemi Osinbajo da kuma, Adams Oshiomhole a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa Abuja

- Babbar jam’iyyar adawar kasar ta bayyana abunda shugaban kasar yayi tare da sauran shugabannin jam’iyya mai mulki a matsayin yaudara

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kawar Kirsimeti da yayi a matsayin taya kiristoci bikin Kirsimeti.

Buhari yayi wakar Kirsimeti ne tare da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da kuma shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa Abuja.

Da take martani akan haka, babbar jam’iyyar adawar kasar ta bayyana abunda shugaban kasar yayi tare da sauran shugabannin jam’iyya mai mulki a matsayin yaudara.

2019: Yadda Buhari, Osinbajo da Oshiomhole suka yaudari yan Najeriya a ranar Kirisimeti - PDP

2019: Yadda Buhari, Osinbajo da Oshiomhole suka yaudari yan Najeriya a ranar Kirisimeti - PDP
Source: Twitter

A wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter, kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa allai Buhari yayi wakar Kirsimeti ne domin a sake zabar shi.

KU KARANTA KUMA: Neman kudi da sunan Buhari - Fadar shugaban kasa ta gargadi masu rike da mukaman siyasa

Ya rubuta: “Yan Najeriya sun yi bikin Kirsimeti a Disamba 2015, 2016 da 2017 amma @MBuhari bai san da wakokin Kirsimeti ba.

“Sai gashi yan kwanaki 50+ zuwa zaben s09, inda yake neman tazarce, @MBuhari ya tuna da wakar Kirsimeti harma ya rera ta; Yaudara ne.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel