Jam’iyyar APC ta tarbi masu sauya sheka daga PDP a Kaduna

Jam’iyyar APC ta tarbi masu sauya sheka daga PDP a Kaduna

- Jam’iyyar APC ta tarbi maso sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Kudancin jihar Kaduna

- Tsoffin yan PDP din sun sauya sheka ne a lokacin da ta kaddamar da kamfen din APC a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a da ke jihar Kaduna

- APC ta sha alwashin tafiya da sabbin mambobin nata ba tare da nuna wariya ba

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kudancin jihar Kaduna ta tarbi manyan yayan yankin a lokacin da ta kaddamar da kamfen dinta a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a da ke jihar Kaduna.

Jam’iyyar APC ta tarbi masu sauya sheka daga PDP a Kaduna

Jam’iyyar APC ta tarbi masu sauya sheka daga PDP a Kaduna
Source: Depositphotos

Masu sauya sheka sun samu kyakyawar tarba daga shugaban APC a jihar, Air Commodore Emmanuel Jekada (rtd), Dr. Hadiza Balarabe wacce ta kasance mataimakiyar El-Rufai a zabe mai zuwa da kuma darakta janar na kungiyar kamfen din El-Rufai, Mista Ben Kure.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban APC a jihar ya bayyana sauya shekar a matsayin alamu na cewa APC na kara samun farin jini da shahara a kudancin Kaduna, inda yayi alkawarin cewa jam’iyyar zata tafi da kowa sannan ba zata nuna wariya ba.

KU KARANTA KUMA: Ko kadan shugaba Buhari ba ya karya – Ministar kudi

A nata bangaren, Dr. Balarabe ta bayyana cewa mata sun amfana matuka daga gwamnatin El-Rufai a bangaren nade-naden mukaman siyasa da kuma manyan ayyuka a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel