Tarin farin ciki a APC yayinda mambobin PDP suka sauya sheka a mahaifar Saraki

Tarin farin ciki a APC yayinda mambobin PDP suka sauya sheka a mahaifar Saraki

Mambobin jam’iyyun siyasa da daban-daban ciki harda na babbar jam’iyyar adawa wato Peoples Democratic Party (PDP) sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Omu-Aran, jihar Kwara.

Akalla mutane 5,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban a yankin kudancin Kwara ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Omu-Aran, jihar Kwara lokacin wani gangami na jam’iyyar.

Mafi akasarin masu sauya shekar daga babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) suke. Bayan an tarbe su, an kuma basu katin zama yan APC.

Tarin farin ciki a APC yayinda mambobin PDP suka sauya sheka a mahaifar Saraki

Tarin farin ciki a APC yayinda mambobin PDP suka sauya sheka a mahaifar Saraki
Source: Depositphotos

Wani jigon PDP, Dr Seyi Adigun wanda ya sauya sheka a yankin Ajase Ward 2 da ke karamar hukumar Irepodun yace: “Duk wani mutun mai tunani ko dan siyasa ya zama dole ya san lokacin da ya kamata ya tsaya ko ya fice sannan kuma ni abunda na sani shine APC son ci gaban yan Najeriya ne a zuciyarta. Na yarda cewa a duk wani zabe na gaskiya da amana kamar wanda akayi a waccan zaben APC ce za ta yi nasara."

Hakazalika, Mista Dare Bamkole, wani shugaban masu sauya sheka daga karamar hukumar Oke-Ero kuma tsohon hadimin Gwamna Abdulafatah Ahmed yace sauya shekarsu nada nasaba da kokarin jam’iyyar kuma APC da mutane sun ji dadin hakan.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kira Sarkin Zamfara, ya nuna bakin ciki akan hare-haren yan fashi

Shugaban APC a jihat, Mista Bashir Bolarinwa yayinda ya tarbi masu sauya shekar yace: “abu mafi muhimmanci shine cewa kada mambobin jam’iyyarmu su hana kansu bacci akan wani hukunci. Ina so ku gane cewa dukkanin yan takararmu a zaben 2019 na nan daram-dakam kuma ni ina nan a matsayina na shugaban APC, inji shi.

Kamfen din ya samu halartan manyan magoya bayan ja’iyyar daga sassa daban-daban na yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel