2019: Mu zuba mu gani Buhari ba zai zamo shugaban kasa ba – Buba Galadima

2019: Mu zuba mu gani Buhari ba zai zamo shugaban kasa ba – Buba Galadima

- Buba Galadima ya bayyana cewa ranar 29 ga watan Mayu, 2019 na gabatowa, kuma ba Buhari za a rantsar ba

- Ya ce zuwa ranar damokradiya mai zuwa a Najeriya, Buhari ya rigada ya mika mulki Atiku

- Jigon kasar yace aiki na farko da ‘shugaban kasa’ Atiku Abubakar zai yi wato sanya hannu a dokar zabe

Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa ranar 29 ga watan Mayu, 2019 na gabatowa, kuma ba shugaban kasa Muhammadu Buhari za a rantsar ba.

Galadima ya ce zuwa ranar damokradiya mai zuwa a Najeriya, Buhari ya rigada ya mika mulki ga dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

2019: Mu zuba mu gani Buhari ba zai zamo shugaban kasa ba – Buba Galadima

2019: Mu zuba mu gani Buhari ba zai zamo shugaban kasa ba – Buba Galadima
Source: Depositphotos

Da yake martani akan rashin sanya hannu da Buhari yaki yi kan dokar zabe, Galadima yace, “Ina raddi ga shugaban kasar yace zai mai ba gwamnatin gaba, babu shakka, Allah zai amsa addu’ansa, zuwa 29 ga watan Mayu, ba zai kasance a matsayin shugaban kasar Najeriya ba.”

Jigon kasar ya ci gaba da cewa idan PDP tazo, zai zamo aiki na farko da shugaban kasa Atiku Abubakar zai yi wato sanya hannu a dokar zabe.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kira Sarkin Zamfara, ya nuna bakin ciki akan hare-haren yan fashi

Galadima ya ci gaba da Magana akan yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyun siyasa suka shiga saboda zaben kasar mai zuwa.

Yace Atiku dan damokradiyya ne wanda ya yarda da doka, inda ya bayyana cewa ana zaman lafiya ne akan adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel