Yanzu Yanzu: Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari sun kona gidaje kusa da garin Chibok

Yanzu Yanzu: Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari sun kona gidaje kusa da garin Chibok

- Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a karamar hukumar Chibok da ke jihar Borno

- Sun kuma kone wani kauye sukutum a kusa da garin Chibok

- An tattaro cewa sun kuma tafi da kayayyakin abinci bayan sun budewa jama’a wuta a kauyen

Wasu da ake zargin yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari sannan suka kone wani kauye sukutum a karamar hukumar Chibok da ke jihar Borno a safiyar ranar Laraba, 26 ga watan Disamba wasu majiyoyi na yan banga suka bayyana.

Harin ya faru ne a kauyen Mbolakel, kusa da garin Chibok da misalin karfe 1:00 na tsakar dare.

Yanzu Yanzu: Yan ta’adda Boko Haram sun kai hari sun kona gidaje kusa da garin Chibok

Yanzu Yanzu: Yan ta’adda Boko Haram sun kai hari sun kona gidaje kusa da garin Chibok
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta’addan na ta harbi ba kakkautawa, sun kuma raunata wasu mutane da ba’a san adadinsu ba sannan suka kona dabbobi yayinda suka tafi da kayayyakin abinci.

An tattaro cewa akalla gidaje sama da 25 aka kona lokacin da maharani suka kai farmaki.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

A cewar majiyar, mazauna kauyen sun gudu zuwa daji domin tsira, inda wata tsohuwa ta kone fiye da tunani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel