Ko kadan shugaba Buhari ba ya karya – Ministar kudi

Ko kadan shugaba Buhari ba ya karya – Ministar kudi

- Ministar kudi, Zainab Ahmed ta kare ubangidanta Buhari kan ayyukan da ya ce gwamnatinsa na aiwatarwa a yayinda yake gabatar da kasafin kudin 2019

- Zainab ta bayyana cewa Buhari ba ya karya ko kadan

- Ta ce duk abunda shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta aiwatar toh tabbass hakan yake

Ministar kudi, Zainab Ahmed ta kare ubangidanta shugaban kasar Muhammadu Buhari kan ayyukan da ya ce gwamnatinsa na aiwatarwa a yayinda yake gabatar da kasafin kudin 2019 a gaban majalisar dokokin kasar.

Ministar kudi ta ce babu yadda za a yi Buhari ya yi karya ta hanyar fadin abinda ba gaskiya ba.

Ko kadan shugaba Buhari ba ya karya – Ministar kudi

Ko kadan shugaba Buhari ba ya karya – Ministar kudi
Source: Depositphotos

Tace: "Shugaban kasa mutum ne mai gaskiya kuma tsayayye, ba yanda za a yi ya ce an yi abu alhalin ba a yi shi ba."

Ta kara da cewa dukkanin ayyukan da shugaban kasar ya fada suna cikin kasafin kudin shekarar 2018, wanda zai tsaya a watan Yunin shekarar 2019.

Ta kuma ce an sake sanya ayyukan cikin kasafin kudin shekarar 2019, domin ganin ayyukan sun kammalu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Boko Haram sun fille kan mai tsaron Gwamna Gaidam

An dai samu hatsaniya a lokacin da Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a zauren majalisar dokokin.

Inda wasu wakilan majalisar suka rinka katsalandan a lokacin da shugaban kasar ke jawabi, musamman a lokacin da yake bayani kan nasarorin gwamnatinsa.

Sun rinka cewa 'karya', ko 'a ina?', wasu kuma na cewa 'ba haka ba ne.'

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel