Buhari ya kira Sarkin Zamfara, ya nuna bakin ciki akan hare-haren yan fashi

Buhari ya kira Sarkin Zamfara, ya nuna bakin ciki akan hare-haren yan fashi

- Shugaba Buhari ya kira Sarkin Maradun da ke Zamfara, Alhaji Garba Tambari akan wayar tarho

- Ya nuna bakin ciki akan rasa rayuka da asarar dukiyoyi da aka yi sakamakon hare-haren yan fashi

- Buhari yayi alkawarin cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ganin tayi duk abunda ya kamata domin tsare kawo karshen irin wadaddan hare-haren

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 25 ga watan Disamba ya kira Sarkin Maradun da ke Zamfara, Alhaji Garba Tambari akan wayar tarho, ya nuna bakin ciki akan rasa rayuka da asarar dukiyoyi da aka yi sakamakon hare-haren yan fashi.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi daga babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, a Abuja a ranar Talata.

Buhari ya kira Sarkin Zamfara, ya nuna bakin ciki akan hare-haren yan fashi

Buhari ya kira Sarkin Zamfara, ya nuna bakin ciki akan hare-haren yan fashi
Source: Twitter

Shugaba Buhari yace yana matukar bakin ciki da rasa rayuka da asarar dukiyoyi bayan hare-haren da yan ta’addan suka kai.

Ya bukaci Sarkin da yayi jaje ga mutanensa, da al’umman kasar baki daya akan wannan abun bakin ciki da ya riske su.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

Ya sake jadadda cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ganin tayi duk abunda ya kamata domin tsare jihar da ma kasa baki daya sannan kuma za ta kawo karshen irin wadaddan hare-haren.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel