Gwamnatin Buhari na yunkurin kafa dokar ta baci a Zamfara – Inji Fayose

Gwamnatin Buhari na yunkurin kafa dokar ta baci a Zamfara – Inji Fayose

- Ayo Fayose yace ana shirin hana ayi zaben sabon Gwamna a Jihar Zamfara

- Tsohon Gwamnan yace Buhari zai yi haka ne don a hana APC takara a 2019

- Fayose yace a yanzu zaben shugaban kasa kurum Buhari ya ke so ayi a Jihar

Gwamnatin Buhari na yunkurin kafa dokar ta baci a Zamfara – Inji Fayose

Fayose yace ba za ayi zaben gwamna da ‘yan Majalisun dokoki a Zamfara ba
Source: Depositphotos

Mun samu labari daga jaridar nan ta Vanguard cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin kakaba dokar ta-baci a jihar Zamfara da sunan inganta sha’anin tsaro domin a dage zaben Jihar.

Ayodele Fayose, wanda kwanan nan ya bar kujerar mulki, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta kyankyashi wannan danyan aiki ne bayan Hukumar zabe na kasa watau INEC ta tabbatar da cewa APC za tayi takara a jihar Zamfara ba.

KU KARANTA: Buhari ya gaza inganta sha'anin tsaro a Najeriya – Bukola Saraki

Mista Fayose yake cewa ana shirin hana yin zaben gwamna a Zamfara a 2019, inda yace gwamnatin Najeriya za ta fake da sunan rashin tsaro ne domin cin ma wannan mugun manufa. Fayose yayi wannan jawabi ne da hannun sa a jiya.

Jagoran na yakin neman zaben Atiku Abubakar a yankin Kudu maso yamma ya bayyana cewa a 2019, zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun Tarayya kurum ake so ayi, tun da an haramtawa APC fitar da ‘Dan takara a zaben mai zuwa.

A cewar Ayodele Fayose, za a dage zaben gwamna da majalisun jihar zamfara ne sai a cikin watan Mayu. Tsohon gwamnan na PDP ya nemi gwamnatin Buhari ta ajiye wannan batu, ba mutanen Zamfara hakurin masifar da ta jefa ta a ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel