Yanzu-Yanzu: Sojoji 13, dan sanda 1 sun mutu yayin sabon artabu da 'yan Boko Haram

Yanzu-Yanzu: Sojoji 13, dan sanda 1 sun mutu yayin sabon artabu da 'yan Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya ta ayyana cewa jami'an ta akalla 13 ne da kuma wani jami'in 'yan sanda suka rasa rayukan su yayin wani kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka kai masu a sansanin su dake daya daga cikin garuruwan jihar Borno.

Mataimakin babban Daraktan hulda da jama'a na rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Yanzu-Yanzu: Sojoji 13, dan sanda 1 sun mutu yayin sabon artabu da 'yan Boko Haram

Yanzu-Yanzu: Sojoji 13, dan sanda 1 sun mutu yayin sabon artabu da 'yan Boko Haram
Source: UGC

KU KARANTA: Wata mata ta rika aman sabbin kudade a Najeriya

Legit.ng Hausa ta samu cewa Kanal Onyema Nwachukwu ya kara da cewa mummunan lamarin ya auku ne lokacin da rundunar ta tura jami'an ta sintiri a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Ya kara da cewa dakarun nasu sun yi iya bakin kokarin su suga cewa sun samu galaba akan 'yan ta'addan amma Allah bai nufa ba har dai suka rasa ran na su.

Amma sai dai Kanal Onyema Nwachukwu ya bayar da tabbacin cewa za su kara kaimi wajen ganin sun kakkabe dukkan sauran 'ya ta'addan daga maboyar su a ko ina ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel