Zan yi takarar shugaban kasa a 2023 - Rochas Okorocha

Zan yi takarar shugaban kasa a 2023 - Rochas Okorocha

- Gwamna Rochas Okorocha ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa a 2023

- Yace shine zai zamo shugaban Igbo na farko da za a zaba a mulkin farin hula a 2023

- Ya bayyana kanshi a matsayin madogaran dukkanin yan Igbo sannan kuma mutun daya da zai iya dinke barakar hadin kai

Gwamna Rochas Okorocha ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa a 2023, sannan a cewar gwamnan na jihar Imo, shine zai zamo shugaban Igbo na farko da za a zaba a mulkin farin hula a 2023.

Rochas Okorocha wanda ya bayyana kanshi a matsayin madogaran dukkanin yan Igbo sannan kuma mutun daya da zai iya dinke barakar hadin kai, fahimta da zaman lafiya domin cimma shugabancin kasa na Igbo a 2023.

Zan yi takarar shugaban kasa a 2023 - Rochas Okorocha

Zan yi takarar shugaban kasa a 2023 - Rochas Okorocha
Source: Depositphotos

Ya kaddamar da kudirin nasa ne a yayinda ya karbi bakoncin mambobin yankin Orlu a ofishin sa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya mayar wa Aisha martani a kan zargin ana juya shi

Gwamnan na jihar Imo ya ci gaba da bayyana cewa ana yi masa makarkashiya ne saboda masu adawa dashi sun ga cewa shine dan Igbo da baida kabianci ko kadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel