An hurowa shugaba Buhari wuta saboda ya rera wakar kirisimeti

An hurowa shugaba Buhari wuta saboda ya rera wakar kirisimeti

Wasu 'yan kasar Najeriya sun hurowa Shugaban Muhammadu Buhari wuta saboda ya rera wakar kirisimeti yana taya kiristocin Najeriya murna musamman ma a wannan lokacin da wasu a jihar Zamfara ke fama da rashin tsaro.

A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallafa a shafin shi na Twitter, an ga Buhari ya rera wakar Kirsimeti tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a kuma shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.

An hurowa shugaba Buhari wuta saboda ya rera wakar kirisimeti

An hurowa shugaba Buhari wuta saboda ya rera wakar kirisimeti
Source: Twitter

KU KARANTA: An ga wata mata tana aman sabbin kudade a Najeriya

Legit.ng Hausa ta samu cewa sun rera wakar a tsaye Buhari yana tsakiya cikin murna da murmushi da juna. Baya ga bidiyon da ya wallafa a Twitter, shugaba Buhari kuma ya taya 'yan Najeriya murnar bikin Kirsimeti.

Bidiyon ya samu tsokaci kusan 1,000 inda shugaba Buhari ya sha yabo da suka. Wasu sun ji dadin sakon na taya murna, yayin da wasu kuma suka ce siyasa ce kawai saboda zabe na karatowa, domin shekaru uku a baya na mulkinsa ba su ga shugaban yana rera wakar kirsimeti ba.

Ga dai bidiyon nan kamar yadda aka wallafa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel