Buhari ya mayar wa Aisha martani a kan zargin ana juya shi

Buhari ya mayar wa Aisha martani a kan zargin ana juya shi

- Shugaba Buhari ya mayar da martani ga zargin Aisha, uwargidansa da wasu mutane da ke cewa wasu daban ne ke juya gwamnatinsa

- Buhari ya kalubalance su dasu fito su fadi abubuwan da ba shine yake aiwatarwa ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga zargin Aisha, uwargidansa da wasu mutane da ke cewa wasu daban ne ke juya gwamnatinsa.

Lokuta da dama uwargidan shugaban kasar ta sha fadin cewa wasu na yiwa shugaban kasar shigar gaban hantsi wajen hana shi yin aiki yadda ya so yi.

Buhari ya mayar wa Aisha martani a kan zargin ana juya shi

Buhari ya mayar wa Aisha martani a kan zargin ana juya shi
Source: Facebook

Da take jawabi a wani taron shugabanci a Abuja a farkon wannan wata, Aisha ta kalubalanci yan Najeriya da su yaki wasu mutane biyu zuwa uku da suka hana wannan gwamnatin rawar gaban hantsi.

A wani hira tare da muryar Amurka, Shugaba Buhari ya mayar da martani ga zargin.

KU KARANTA KUMA: Wata yar'uwa Musulma ta kawata gidan fasto don bikin Kirisimeti a Kaduna

Da aka tambaye shi akan na kewaye dashi da mutane k eta Magana a kansu ciki harda uwargidansa wajen ta nemi a yake su a kwanaki shugaban kasar yace:

“Wannan matsalarta ne... Hakan ya nuna cewa ni dan damokradiya ne na usuli... abunda suke fadi ya sha banban da abunda ke faruwa. Su fito su fadi wadannan abubuwan da suke ganin cewa wasu ne ke gudanarwa. Abunda wadannan mutanen ke tursasa ni yi. Su ambaci abu daya kawai."

Shugaban kasar ya kalubalanci sauran mutane dake zargin cewa akwai wasu da ke gudanar da gwamnatinsa dasu fito su kare kansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel