Akwai wani shiri da ake na yi mun alluran mutuwa a ranar Kirsimeti – Dino Melaye

Akwai wani shiri da ake na yi mun alluran mutuwa a ranar Kirsimeti – Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye na jihar Kogi ya koka kan cewa ana shirya munakisan kama shi a ranar Kirsimeti sannan a kashe shi

- Dan majalisan daga Kogi yayi ikirarin cewa ana shirin yi masa alluran mutuwa

Sanata Dino Melaye na jihar Kogi ya koka ga sufeto-janar na yan sanda, Ibrahim Idris, inda yayi ikirarin cewa ana shirya munakisan kama shi a ranar Kirsimeti sannan a kashe shi.

Akwai wani shiri da ake na yi mun alluran mutuwa a ranar Kirsimeti – Dino Melaye

Akwai wani shiri da ake na yi mun alluran mutuwa a ranar Kirsimeti – Dino Melaye
Source: Depositphotos

A wani rubutu da ya wallafa a ranar Talata, 25 ga watan Disamba, dan majalisan daga Kogi yayi ikirarin cewa ana shirin yi masa alluran mutuwa.

Yace: “Akwai wani shiri daga IGP na kama nu a yau sannan ayi mani allura mutuwa. Tuni an turo jami’ai. An tsige kwamishinan Kogi da wasu. Yan Najeriya ku zuba idanu."

KU KARANTA KUMA: 2019: Ba zan taba yaudarar Atiku ba – Dankwambo

A wani lamari na daban mun ji cewa Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kai ziyarar jaje jihar Zamfara kafin ya je Akwa Ibom don kaddamar da kamfen dinsa.

Legit.ng ta rahoto da farko cewa wasu yan fashi a ranar Laraba, 19 ga watan Disamba sun kai farmaki garuruwa uku a karsamar hukumar Birnin Magaji na jihar Zamfara, inda suka kashe mutane da dama.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai wadanda ke aiki a gonakinsu lokacin da aka far masu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel