Surukin Shugaban kasa ya ba wasu kamfanonin da ba su cancanta ba kwangiloli

Surukin Shugaban kasa ya ba wasu kamfanonin da ba su cancanta ba kwangiloli

Mun ji cewa Jaridar Premium Times ta bankado yadda shugaban hukumar BDCA mai lura da kan iyakokin Najeriya watau Junaidu Abdullahi ta rika sabawa dokar aiki na kasa wajen bada wasu kwangiloli.

Surukun Shugaban kasa ya ba wasu kamfanonin da ba su cancanta ba kwangiloli

Ana zargin Hukumar BCDA da nuna son kai wajen raba kwangiloli
Source: Twitter

Kamfanin na BDCA ya rika bada kwangiloli ne domin ayi wasu ayyuka a fadin kasar nan kwanakin baya. Yanzu haka Junaidu Abdullahi, wanda ya taba auren babban ‘Diyar Shugaban kasa Buhari ne yake rike da Hukumar ta BDCA.

Binciken da jaridar tayi ya nuna cewa daga cikin kamfanonin da BDCA ta ba kwangila akwai wadanda ba su cancanta ba. Jaridar tace an nuna son kai wajen zaben kamfanonin da aka rabawa kwangilolin na sama da Naira Biliyan 1.3

KU KARANTA: Gwamnan PDP ya saduda ya ba Shugaba Buhari wajen taron kamfen

Daga cikin sharudan da aka gindaya kafin a ba kamfanin kwangila a hukumar, dole sai an bada takardun nuna shaidar biyan haraji kuma su ke juya akalla Miliyan 50 a duk shekara. Kamfanoni fiye da 30 su ka nemi a ba su kwangila.

Sai dai kuwa kamfanin Estivus Nigeria Limited yana cikin wadanda aka ba wannan kwangila duk da bai cika sharudan da aka gindaya ba. Junaidu Abdullahi yayi kokarin nuna cewa sun yi rangwame ne a game da sharudan da aka sa.

Premium Times tace hukumar dai ta yi watsi da sauran kamfanonin da su ka cika sharudan yin wannan aiki, amma su ka zabi kamfanin Estivus Limited. Wannan son kai da aka nuna ya sabawa dokokin aiki da kuma tsarin mulkin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel