Yan bindiga sun kashe shugaban APC, wasu 5 sannan suka sace basarake a Rivers

Yan bindiga sun kashe shugaban APC, wasu 5 sannan suka sace basarake a Rivers

- Yan bindiga sun kashe Shugaban jam’iyyar APC a Onne, karamar hukumar Eleme, jihar Rivers, Jonah Chu

- Sun kuma kashe mutane biyar a farmakin da suka kai a ranar Lahadi

- Masu garkuwa da mutane sun sace sarkin garin Rumuepirikom a karamar hukumar Obio/Akpor da ke jihar Rivers, Eze Anthony Owabie a ranar Lahadi

Wasu yan bindiga sun kashe Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a Onne, karamar hukumar Eleme, jihar Rivers, Jonah Chu.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai farmaki Onne sannan suka kashe shi.

Hakan na zuwa ne yayinda yan bindigan suka kashe mutane biyar a garin Adada-Odua da ke, karamar hukumar Abua/Odua a jihar.

Yan bindiga sun kashe shugaban APC, wasu 5 sannan suka sace basarake a Rivers

Yan bindiga sun kashe shugaban APC, wasu 5 sannan suka sace basarake a Rivers
Source: Depositphotos

Wata majiya ta bayyana cewa shugaban kamfen din Tonye Cole Volunteers Group a wanda shine shugaban APC na yankin 9 na daga cikin mutan biyar da aka kashe a daren ranar Lahadi.

Sai dai ba’a ji daga bakin kakakin yan sandan jihar ba a lokacin wannan rahoton.

A halin da ake ciki, an sace sarkin garin Rumuepirikom a karamar hukumar Obio/Akpor da ke jihar Rivers, Eze Anthony Owabie a ranar Lahadi.

An tattaro cewa an sace Owabie a hanyar Ozuzu-Etche da ke karamar hukumar Etche na jihar.

KU KARANTA KUMA: 2019: Za mu zaba tsakanin Buhari da Atiku a wannan makon - Kungiyar Miyetti Allah

Daga bisani anga motarsa a kan hanyar dauke da jurwayin jini.

Yan sanda sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargin suna da nasaba da garkuwan sannan ana kokarin ganin an sake shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel