Gwamnatin Najeriya tana biyan tallafin mai N20 a kan kowane lita domin fetur ya tsaya a N145 - NNPC

Gwamnatin Najeriya tana biyan tallafin mai N20 a kan kowane lita domin fetur ya tsaya a N145 - NNPC

- Gwamnatin Buhari ta na kashe kudi wajen biyan tallafin man fetur

- Shugaban Kamfanin NNPC yace a duk lita Gwamnati tana kashe N20

- Yanzu an samu saukin abin da ake kashewa a kan tallafin man fetur

Gwamnatin Najeriya tana biyan tallafin mai N20 a kan kowane lita domin fetur ya tsaya a N145 - NNPC

Shugaba Buhari yana biyan man tallafin man fetur
Source: UGC

Mun ji cewa Dr. Maikanti Baru wanda shi ne shugaban darektan kamfanin man Najeriya nan NNPC, ya bayyana cewa kudin da gwamnatin Najeriya ta ke biya wajen bada tallafin man fetur ya ragu a halin yanzu daga N80 kuma zuwa N20.

Maikanti Baru ya bayyana mana wannan ne a cikin Garin Abuja lokacin da yake wani zagaye zuwa gidajen mai tare da ma’aikatan DPR da kuma Jami’an tsaro na NSCDC domin ganin an samu isasshen mai a fadin kasar a wannan lokaci.

KU KARANTA: Babban Gwamnan PDP ya yabawa Gwamnatin Shugaban kasa Buhari

Darektan na NNPC yayi amfani da wannan dama inda ya bayyanawa jama’a adadin kudin da ake kashewa domin ganin man fetur bai kara farashi daga N145 ba. GMD na NNPC yace kudin da ake kashewa kan tallafin man fetur ya sauka kasa.

Maikanti Baru yace a yanzu da ake saida gangar man fetur a kan $60, abin da ake biya domin a cigaba da saida litar mai a kan N145, bai wuce N20 zuwa N25 ba. A baya dai har ta kai gwamnatin kasar ta na cika N80 domin kar fetur din ya kara kudi.

Dr. Baru ya kuma yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganin ba ayi fama da wahalar man fetur a lokutan bukin kismet kamar yadda aka saba a baya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel