2019: Ba zan taba yaudarar Atiku ba – Dankwambo

2019: Ba zan taba yaudarar Atiku ba – Dankwambo

- Gwamna Ibrahim Dankwambo ya yi watsi da rade-radin cewa yana hada kai da gwamna Aminu Tambuwal domin su yaudari Atiku

- Dankwambo ya bayar da tabbacin cewa yana tare da tsohon mataimakin shugaban kasar, sannan yayi alkawarin kawo masa yankin arewa maso gabas baki daya a zabe mai zuwa

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwambo ya yi watsi da rade-radin cewa yana hada kai da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal domin su yaudari dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar.

2019: Ba zan taba yaudarar Atiku ba – Dankwambo

2019: Ba zan taba yaudarar Atiku ba – Dankwambo
Source: UGC

A cewar jaridar ThisDay, Dankwambo ya bayar da tabbacin cewa yana tare da tsohon mataimain shugaban kasar, sannan yayi alkawarin kawo masa yankin arewa maso gabas baki daya a zabe mai zuwa.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan jihar Gombe wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar kamfen din Atiku a arewa maso gabas yayi Magana ne ta hannun babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Alhaji Junaid Usman Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Saad tsohon gwamnan Jigawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Kakakin gwamnan ya kara da cewa ubangidansa na da baki sosai a fadin arewa maso gabas, kasancewarsa wanda ya jajirce ya tsaya a PDP kuma wanda ya samu tarin nasarori a shekaru takwas da yayi yana mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel