Zaben 2019: Atiku ya sake tika Buhari da kasa a wani zaben gwaji na yanar gizo

Zaben 2019: Atiku ya sake tika Buhari da kasa a wani zaben gwaji na yanar gizo

Kimanin wata daya kacal bayan fara yayin neman zaben shekarar 2019, shugaban kasa mai ci a halin yanzu, Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a wani zaben gwaji na yanar gizo.

A karshen zaben, Atiku Abubakar din ne dai ya samu kuri’u kaso 98 cikin 100 yayin da shi kuma Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kaso 2 kacal na kuri'un da aka kada.

Zaben 2019: Atiku ya sake tika Buhari da kasa a wani zaben gwaji na yanar gizo

Zaben 2019: Atiku ya sake tika Buhari da kasa a wani zaben gwaji na yanar gizo
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An sake kai kazamin hari a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa tsohon gwamnan jihar Cross River kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Mista Donald Duke da kuma yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar Allied Congress Party kuma tsohuwar ministar ilimi Dr Oby Ezekwesili ba su samu kuri’a ko daya ba.

Wani nazari da akayi ya nuna cewa gaba daya kuri’un da aka kada 10,496 ne inda Atiku ya samu kuri’u 10,286, sannan shugaba Buhari ya zo na biyu inda ya samu 2,090 yayinda Duke da Ezekwesili basu samu ko daya ba.

A wani labarin kuma, dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a daya daga cikin jam'iyyun adawa ta All Progressives Grand Alliance (APGA) mai suna Alhaji Sani Shinkafi yace mabiyan sa su zabi shugaba Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel