An sake kai hari a ofishin kamfe na APC a kudu, an kona musu motoci

An sake kai hari a ofishin kamfe na APC a kudu, an kona musu motoci

- An kaima ofishin yakin neman zaben APC na jihar Enugu hari

- Maharan sun kone motoci biyu a harabar

- A halin yanzu mista Ogara ya maka jam'iyyar APC kotu

An sake kai hari a ofishin kamfe na APC a kudu, an kona musu motoci

An sake kai hari a ofishin kamfe na APC a kudu, an kona musu motoci
Source: Twitter

An kaiwa ofishin yakin neman zaben APC na jihar Enugu hari. Hakan ya kai ga konewar motoci biyu.

Ofishin yakin neman zaben George Tagbo Ogara,daya daga cikin masu ikirarin su ke da tikitin kujerar gwamnan jihar Enugu karkashin jam'iyyar APC.

Maharan sun kone motocin kamfen har guda biyu.

Ganau ba jiyau ba sun ruwaito cewa yan kwana kwana sun je gurin da gaggawa inda suka kashe wutar.

Mista Ogara yace da wani abu mai fashewa suka yi amfani yayin harin, wanda hakan ya kawo sanadin konewar motocin.

Mista Ogara, wanda yace yana Legas a yayin faruwar abun yace bai san ta inda aka kawo harin ba

"Abubuwa masu fashewa ba abinda farar hula zasu iya shiga bane. Yan sanda da DSS zasu binciki al'amarin."

DUBA WANNAN: Yadda gwamnatin tarayya ta ɓatar da $322m da ta kwato a hannun iyalan Abacha - Garba Shehu

Mista Ogara dake ikirarin cewa shine Dan takarar da APC reshen jihar Enugu ya kai jam'iyyar kotu sakamakon wallafa sunan tsohon sanata Ayogu Eze a matsayin Dan takarar su.

An sanya sauraran karar a babban kotu dake Abuja a ranar 10 ga watan janairu.

Mai magana da yawun yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar al'amarin. Yace kuma ana cigaba da bincike.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel