Buhari zai fara kamfen din 2019 a Akwa Ibom

Buhari zai fara kamfen din 2019 a Akwa Ibom

- Shugaba Buhari a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba zai fara kamfen dinsa na neman tazarce a Uyo, babbar birnin jihar Akwa Ibom.

- Sanata Ita Enang, babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dokoki (majalisar dattawa) ya bayyana hakan

- Jam’iyyar za ta yi amfani da damar wajen gabatar da tutar jam’iyyar ga yan takarar gwamna na APC a Akwa Ibom, Cross River da Delta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba zai fara kamfen dinsa na neman tazarce a Uyo, babbar birnin jihar Akwa Ibom.

Sanata Ita Enang, babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dokoki (majalisar dattawa) ya bayyana hakan a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba yayin da yake jawabi ga manema labarai a Uyo.

Buhari zai fara kamfen din 2019 a Akwa Ibom

Buhari zai fara kamfen din 2019 a Akwa Ibom
Source: Depositphotos

Enang ya ayyana cewa shugaban kasa zai kasance a jihar tare da shugaban jam’iyyar na kasa Kwamrad Adams Oshiomhole da kuma babban jigon jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da damar wajen gabatar da tutar jam’iyyar ga yan takarar gwamna na APC a Akwa Ibom, Cross River da Delta.

KU KARANTA KUMA: Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo

A wani lamari na daban, Kungiyar Fulani makiyaya, Miyetti Allah ta bayyana cewa za ta sanar da dan takararta na shugaban kasa kafin karshen wannan makon.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa babban sakataren kungiyar, Saleh Alhassan, ya fadi hakan a wani hira da musamman da akayi dashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel