Zamfara: Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama umarnin gaggawa

Zamfara: Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama umarnin gaggawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Abubakar Baba Sadique, umarnin gaggauta zuwa jihohin Sokoto da Zamfara a yau, Talata, da gobe, Laraba, domin yin kiyasin ta'adin da 'yan ta'adda suka yi a sassan jihohin.

A jawabin da Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce shugaban rundunar sojin saman zai shafe tsawon kwanaki biyu na hutun bikin Kirsimeti a jihohin.

An kashe dubban mutane a cikin shekaru biyu sakamakon aiyukan 'yan ta'adda a kauyukan jihar Zamfara.

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da kisan mutane a Birnin Magaji dake karamar hukumar Tsafe da garin Magami dake masarautar Faru a karamar hukumar Maradun da 'yan ta'adda suka yi.

"Wannnan harin ta'addanci a kan bil'adama abun takaici ne da dole mu kawo karshensa," a cewar Buhari.

Zamfara: Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama umarnin gaggawa

Sadique Abubakar
Source: Depositphotos

Da yake mika sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasa 'yan uwa da abokan arziki yayin hare-haren, shugaba Buhari ya yiwa wadanda suka samu raunuka fatan samun sauki da gaggawa.

Kazalika ya bawa mazauna jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna, Neja da Taraba tabbacin cewar gwamnatinsa zata cigaba da kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

DUBA WANNAN: Faifan bidiyo: Jiki magayi, sai mun ja Buhari - Matasan Zamfara

Sakamakon hakan ne ya saka gwamnatin tarayya kafa wata runduna ta jami'an tsaro daban-daban da zata yi aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Buhari ya nuna goyon bayansa ga rundunar 'yan sanda ta kasa bisa tura jami'anta na musamman zuwa jihar Zamfara domin yin maganin masu kai hare-hare. Kazalika ya yabawa rundunar soji bisa tura dakarun soji 1,000 zuwa yankunan arewa ta yamma da

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel