2019: Za mu zaba tsakanin Buhari da Atiku a wannan makon - Kungiyar Miyetti Allah

2019: Za mu zaba tsakanin Buhari da Atiku a wannan makon - Kungiyar Miyetti Allah

- Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana cewa za ta sanar da dan takararta na shugaban kasa kafin karshen wannan makon

- Daga dan takarar APC, Buhari har na PDP, Atiku duk Fulani ne kuma suna kiwo

- A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar makiyaya, a jihar Benue, Garus Gololo ya caccaki Atiku inda ya kira shi a matsayin wanda zai raba kan kasa

Kungiyar Fulani makiyaya, Miyetti Allah ta bayyana cewa za ta sanar da dan takararta na shugaban kasa kafin karshen wannan makon.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa babban sakataren kungiyar, Saleh Alhassan, ya fadi hakan a wani hira da musamman da akayi dashi.

2019: Za mu zaba tsakanin Buhari da Atiku a wannan makon

2019: Za mu zaba tsakanin Buhari da Atiku a wannan makon
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa manyan yan takarar kujerar shugaban kasa, shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) duk Fulani ne kuma dukkaninsu makiyaya ne.

KU KARANTA KUMA: Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo

An tattaro cewa a lokacin da aka tambaye shi wanda kungiyar za su zaba, Alhassa yace, “Za mu yi sanarwa a wannan makon. Za su gudanar da wani taro na manema labarai a Abuja.”

A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar makiyaya, a jihar Benue, Garus Gololo ya caccaki Atiku inda ya kira shi a matsayin wanda zai raba kan kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel