Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo

Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da aiki don zaman lafiya yayinda zaben 2019 ke kara gabatowa

- Ya yi gargadin cewa yan Najeriya ne za su dauki laifi ba Allah ba ida har zaman lafiya yayi kaura daga kasar

- Tsohon shugaban kasar yace halin da kasar ke ciki a yanzu bai da kyau ko kadan

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da aiki don zaman lafiya yayinda zaben 2019 ke kara gabatowa.

Ya yi gargadin cewa yan Najeriya ne za su dauki laifi ba Allah ba ida har zaman lafiya yayi kaura daga kasar.

Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo

Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo
Source: UGC

Jigon kasar ya bayar da shawarar ne a yammacin ranar Lahadi lokacin bikin kirsimeti na 2018 wanda cocin Chapel of Christ the Glorious King (CCKG) ta shirya a dakin karatu na Obasanjo da ke Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.

Ya nuna yakinin cewa 2019 zai zamo shekarar falala ga dukkanin al’umma dama kasar baki daya.

KU KARANTA KUMA: Yakin neman zabe: Osinbajo na burma wuka a cikinsa – Atiku

“Zaman lafiyar kasa na da matukar muhimmanci duba ga yawan rashin tsaro a kasar,” cewar wani jawabi daga kakain Obasanjo, Kehinde Akinyemi.

Tsohon shugaban kasar wanda ya nuna fadin ciki ga taron, yace halin da kasar ke ciki a yanzu bai da kyau ko kadan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel