Wani sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP a Kwara

Wani sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP a Kwara

Mun samu labari daga jaridun Najeriya cewa wani rikici ya barke a jam’iyyar adawa ta PDP a cikin Jihar Kwara inda aka samu wasu da su ka bangare daga jam’iyyar a daidai lokacin da ake haramar zaben 2019.

Wani sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP a Kwara

An samu wadanda su ka balle daga asalin Jam’iyyar PDP a Kwara
Source: Facebook

Ana ta faman rikici a cikin jam’iyyar PDP bayan da Cif Sunday Ivbitoye ya kafa jam’iyyar PDP ta-ware a Jihar Kwara. Ibitoye yace dole su bangare daga uwar jam’iyya domin an gaza shawo kan banbancin da ke tsakanin su a halin yanzu.

Sunday Ivbitoye yake cewa PDP ta na zaune kalau kafin wasu bakin-haure su shigo cikin ta. Cif Ivbitoye ya zargi wadanda su ka dawo PDP kwanan nan daga Jam'iyyar APC da jefa jam’iyyar cikin wannan murdadden hali da ta samu kan ta.

Shugaban ta-waren na PDP yace wannan rigima ce ta sa tsohon shugaban jam’iyyar watau Akogun Iyiola Oyedepo, ya tattara ya koma APC. Sai dai shi Ivbitoye ya sha alwashin karbe PDP daga hannun wadannan sababbin shiga.

KU KARANTA: 2019: Jam’iyyar APC ta shiga cikin rikici a Jihar Kwara

Sakataren yada labarai na PDP a Kwara, Tunde Ashaolu, yayi maza ya fitar da jawabi inda yace babu wata baraka da ta shigo cikin tafiyar PDP. Ashaolu shi ne ainihin kakakin jam’iyyar PDP a Jihar, kuma su na tare ne da Jio Bukola Saraki

Tunde Ashaolu ya kara tabbatar da cewa Honarabul Kola Shittu ne shugaban PDP a Kwara ba kowa ba. Ashaolu ya kuma kara da cewa jam'iyyar PDP ta karbi ragowar ‘Ya ‘yan Akogun Iyiola Oyedepo wadanda su ka ki bin sa zuwa APC.

Kwanaki kun ji yadda PDP ta shawo kan Gwamnan Kwara ya hakura da takarar Sanata da yayi niyya inda aka kyale wanda ke kai ya koma kan kujerar sa. Bukola Saraki yayi hakan ne bayan APC ta sha kasa a zaben Majalisa da aka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel