Yakin neman zabe: Osinbajo na burma wuka a cikinsa – Atiku

Yakin neman zabe: Osinbajo na burma wuka a cikinsa – Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya zargi Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da burma wa kansu wuka a yayin kamfen

- Hakan martani ne ga kira da Osinabajo yayiwa yan Najeriya kan cewa kada su yarda da alkawaran karya

- Atiku yace tunda dai APC ta gaza cika alkawaran zaben 2015 toh kalaman Osinbajo raddi ne a kansu

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya zargi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da burma wa kansu wuka a yayin kamfen.

Yakin neman zabe: Osinbajo na burma wuka a cikinsa – Atiku

Yakin neman zabe: Osinbajo na burma wuka a cikinsa – Atiku
Source: Depositphotos

Atiku, wanda ya yi wannan jawabi ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, na mayar da martani ne ga umurnin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi na cewa yan Najeriya su yi watsi da alkawaran karya yayinda yake gudanar da kamfen din gida-gida a Lagas a ranar Lahadi da ya gabata.

Dan takarar shugaban kasar yace gazawar da suka yi wajen cika alkawaran zaben 2015, mataimakin shugaban kasar na fadama yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kenan a 2019.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2019 zai sha zaman jira har sai bayan zabe – Yan majalisa

A wani lamari na daban mun ji cewa Titi Abubakar, uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ta bayyana rashin jin dadin ta a kan halin da al'ummar Najeriya ke ciki a halin yanzu musamman mutanen yankin Arewa.

A yayin da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta zargi na kusa da Buhari laifi a kan yadda abubuwa ke tabarbarewa a kasar, Titi Abubakar tayi korafi ne a kan yadda talauci ke karuwa da rashin ayyukan yi da rashin lafiya da ke janyo al'umma na mutuwa.

Titi ta koka kan yadda a yanzu 'yan Najeriya suke gaza sayan kayayakin masarufi da abinci idan aka kwantanta da yadda lamura ke tafiya gabanin zuwan shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015 wadd ta ce abin kunya ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel