Hukumar PPRA tayi watsi da zargin wawuran Tiriliyan 1.3 daga kudin IGR

Hukumar PPRA tayi watsi da zargin wawuran Tiriliyan 1.3 daga kudin IGR

Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa Hukumar nan ta PPRA mai lura da farashin kayan man fetur, ta musanya zargin da ake yi mata na cewa ta yin awon gaba da wasu kudi da su ka haura Naira Tiriliyan 1.3.

Hukumar PPRA tayi watsi da zargin wawuran Tiriliyan 1.3 daga kudin IGR

Ana zarin Hukumar PPPRA da karkatar da kudin man fetur
Source: Depositphotos

Hukumar PPPRA ta bayyana cewa maganar cewa ba ta maida kudin da ta tatsa zuwa cikin asusun gwamnatin Najeriya ba gaskiya bane. Wani babban Jami’in Hukumar mai suna Apollo Kimichi ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan.

Darekta Janar na ofishin kasafin kudin Najeriya, Ben Akabueze, shi ne ya zargi wasu hukumomin gwamnatin tarayya irin su PPPRA da wasun su da kin maidawa asusun Najeriya da ke CBN kudin IGR da su ka haura Naira tiriliyan 10.

KU KARANTA: Ala-ka-kai: Abin da ya sa aka gaza kawo karshen rashin wuta a Najeriya

Apollo Kimchi ya maidawa Ben Akabueze raddi inda yace a ko yaushe PPPRA ta kan maidawa gwamnati kashi 25% na kudin da ta samu kamar yadda doka ta ce. Manajan hukumar yace abin da Akabueze yake fada ba gaskiya bane.

Mista Kimchi ya kara da cewa abin da hukumar ta PPPRA ta ke samu a kasar, sam bai kai abin da ofishin kasafin ya bayyana ba. Kimchi ya fitar da wannan jawabi ne a Ranar Litinin dinnan yana mai musanya wannan zargi maras tushe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel