Gwamnatin Buhari ta kawo manufofin da su taimakawa marasa karfi - Dankwambo

Gwamnatin Buhari ta kawo manufofin da su taimakawa marasa karfi - Dankwambo

Manema labaran Najeriya sun rahoto cewa Gwamna Ibrahim Dankwambo na Jihar ya yabawa kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke yi na taba rayuwar talakawan da ke kasar nan.

Gwamnatin Buhari ta kawo manufofin da su taimakawa marasa karfi - Dankwambo

Gwamnan Jihar Gombe ya yabawa Gwamnatin APC
Source: Twitter

Mai girma gwamna Hassan Ibrahim Dankwambo ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari ne a lokacin da yake gabatar da kundin kasafin kudin jihar Gombe na shekarar badi a gaban ‘Yan majalisun dokokin jihar a Ranar Litinin dinnan da ta gabata.

Gwamnan da bakin sa yace ya ga kokarin gwamnatin tarayya na ganin an rage radadin talauci tare da samawa matasa aikin yi a Jihar Gombe. Dankwambo ya kuma ce tsare-tsare irin su YESSO rage yawan marasa aikin yi da ake da su a Gombe.

KU KARANTA: Rikicin cikin gida: Okorocha yayi kaca-kaca da Shugaban Jam’iyyar APC

Ibrahim Dankwambo yake cewa wadannan tsare-tsare da Buhari ya kawo sun fitar da jama’a daga kangin talauci ganin yadda su ka taba rayuwar matasa. A 2019, Dankwambo yace sun ware Biliyan 1.9 domin tallafawa rayuwar matasan jihar sa.

Bugu da kari kuma, gwamnan na PDP wanda yana cikin wadanda su ka nemi takarar shuababan kasa ya kara yabawa kwazon da gwamnatin Buhari tayi wajen kafa hukumar nan ta NEDC da zai agazawa mutanen Yankin Arewa maso gabas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel