MTN zai biya Bankin CBN kudin sulhu har Dalar Amurka Miliyan 52.6

MTN zai biya Bankin CBN kudin sulhu har Dalar Amurka Miliyan 52.6

Labari ya iso mana cewa babban kamfanin nan na sadarwa da ake ji da shi a kaf Nahiyar Afrika watau MTN zai biya Bankin CBN na Najeriya tarar makudan kudi wanda sun haura Dalar Amurka har Miliyan 50.

Tattali: MTN zai biya Bankin CBN tarar Dalar Amurka Miliyan 52.6

Kamfanin MTN zai ba Bankin CBN kudi domin ayi sulhu
Source: Depositphotos

Jaridar nan ta Daily Nigerian mai wallafa labarai a shafunan gizo ta bayyana mana wannan a farkon wannan makon. Jaridar kasar tace kamfanin na MTN ya amince ya biya Najeriya wadannan makudan kudi a dalilin laifin da su kayi.

Bankin CBN, wanda shi ne babban bankin Najeriya, ya nemi kamfanin sadarwan na MTN da su biya gwamnatin Najeriya Dala miliyan 52.6 saboda badakalar takardun wasu satifiket na kamfanin da aka yi ba tare da cika sharuda ba.

KU KARANTA: Binciken yadda MTN ke awon aba biliyoyi daga Najeriya

Bayan doguwar zantawa da kai kawo, an ci ma yarjejeniya tsakanin babban bankin na Najeriya da kuma kamfanin, inda MTN ya amince ya biya wadannan makudan kudi wanda sun haura Biliyan 15 a kudin Najeriya na gida watau Naira.

Kamfanin na MTN ya bayyana wannan ne a Ranar Litinin dinnan inda ya fitar da wani jawabi mai nuna cewa sun cin ma yarjejeniya tsakanin su da gwamnatin Najeriya. An yi wannan zama ne dai a Garin Legas da ke kudancin Najeriya.

A jawanin da aka fitar, MTN ya shirya biyan wannan makudan kudi domin ayi sulhu da Najeriya na sabawa wasu dokoki da aka yi wajen karbar takardun shaida da ke bada dama a shigo da kaya cikin kasar nan da nufin kasuwanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel