Kar a yaudare ku da samun shugabancin kasa - Atiku ya yiwa 'yan yanki kudu maso gabas nasiha

Kar a yaudare ku da samun shugabancin kasa - Atiku ya yiwa 'yan yanki kudu maso gabas nasiha

Biyo bayan kalaman sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga yankin kudu maso gabas a 2023; dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gargadi 'yan yankin kudu da kar su bari a rude su don samun kuri'unsu a zaben 2019.

A jawabin da Kassim Afegbua, kakakin kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP, Atiku ya zargi jam'iyyar APC da yin kasuwancin kujerar shugaban kasa a 2023 domin samun damar cigaba da zama a kujerar mulki.

"A kokarin APC na son boye gazawar ta da kuma makale wa a mulki, jam'iyyar ta fara kasuwanci da kujerar shugaban kasa ta hanyar yiwa sassan kudu alkawarin mika mulki gare su a shekarar 2023.

"Daukar wa yankin kudu maso gabas da yankin kudu maso yamma alkawarin mika masu mulki ya nuna cewar jam'iyyar APC na son yaudarar yankin kudu ne kawai, a saboda haka bai kamata 'yan Najeriya su dauke su da muhimmanci ba," a jawabin Afegbua.

Kar a yaudare ku da samun shugabancin kasa - Atiku ya yiwa 'yan yanki kudu maso gabas nasiha

Atiku
Source: Facebook

A kwanakin baya ne Mustapha, yayin halartar wani taro a Owerri, jihar Imo, a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo, ya yi masu alkawarin cewar shugaba Buhari zai mika masu takara bayan kammala zangonsa a 2023.

DUBA WANNAN: Faifan bidiyo: Jiki magayi, sai mun canja Buhari - Matasan Zamfara sun rera waka yayin zanga-zanga

Kazalika, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shaidawa shugabannin yankin kudu maso yamma cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga yankin a shekarar 2023.

A cewar jam'iyyar PDP, akwai alamar yaudara a alkawuran da shugabannin biyu a gwamnatin Buhari suka yi tare da yin kira ga jama'ar kudu da su yi hankali kar a yaudare su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel