Da duminsa: An damke mutane 23 da makamai a zanga-zangan jihar Zamfara

Da duminsa: An damke mutane 23 da makamai a zanga-zangan jihar Zamfara

Hukumar yan sandan jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa ta damke mutane 23 da makamai cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangan da ya zama rikici a karamar hukumar Tsafe ranan Litinin, 24 ga watan Disamba, 2018.

Kwamishanan yan sandan jihar, Mr Usman Bele, ya bayyanawa manema labarai hakan ne a Gusau bayan an kwantar da tarzomar da matasan suka tayar.

Ya ce abinda yafi baiwa hukumar mamakin shine akwai wasu daga cikin masu zanga-zangan da suke dauke da bindiga suna harabawa domin baiwa mutane tsiri kuma suna kona motocin mutanen da ke sakatariyan karamar hukumar.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe shugaba a jam'iyyar APC a jihar Ribas

Yace: "Duk da cewa ana cigaba da damke mutane a shelkwatar karamar hukumar Tsafe, wadanda aka damke zasu taimaka wajen binciken kama sauran."

Idan zaku tuna, mun kawo muku rahoton cewa rikici ya barke a jihar Zamfara kan cigaban rashin tsaro da ya hallaka daruruwan jama'a a jihar cikin shekaran nan.

Masu zanga-zangan a karamar hukumar Tsafe da ke jihar da safiyar ranan Litinin sun tare babban hanyar Gusau zuwa Zaria da ake bi zuwa jihar Kaduna, Kano da Abuja.

Wani idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa yan zanga-zangan sun lalata hotunan yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar, AbdulAziz Yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel